Gwamnatin tarayya ta bayyana fara biyan ma’aikatan jami’o’i NASU, tare da wadanda suka bar aiki hakkokinsu da suka bi bashi.

Hakan na kunshe ta cikin wata sanarwa da daraktan yaɗa labaran ofishin akanta janar ta ƙasa, Bawa Mokwa ya fitar a yau Asabar.

Sanarwar ta ce tuni aka fara biyan ‘ya’yan kungiyar ma’aikatan jami’o’i ta Kasa NASU.

Acewar sanarwar gwamnatin ta tarayya, ta fitar da kudaden ne domin biyan hakkokin ‘yan fansho da ke karkashin kungiyar ‘yan fansho ta Kasa.

Sanarwar ta kuma sake jaddada kudirin gwamnatin tarayya na kulawa da jindadi da walwalar ma’aikatan Kasar da wadanda suka bar aiki.

Leave a Reply

%d bloggers like this: