Dan takarar shugaban Kasa a Jam’iyyar NNPP Sanata Rabiu Musa Kwankwaso na daya daga cikin masu yin Allah wadai da gurfanarwar da aka yiwa yara masu zanga-zanga a gaban Kotu, tare da sanya musu sharudan beli masu tsauri da kotun ta yi.

Kwankwaso ya bayyana cewa yaran da aka gurfanar din alamomi sun nuna cewa yaran na cikin fama da matsananciyar yunwa da rashin lafiya, amma gwamnatin ba ta yi duba da hakan ba, ta tsare su tsawon wani lokaci, tare da cin zarafinsu, mai makon a magance matsalolin da ƙasar ke fuskanta.
Sanata Rabi’u Kwankwaso ya kuma nuna damuwarsa akan sharudan da kotun ta sanyawa yara , inda ya sharuddan a matsayin cin zarafin ɗan Adam.

Tsohon gwamnan ya ce gurfanar da yaran ya sabawa dokokin kare hakkin dan adam a Kasar.
A karshe Kwankwaso ya bukaci hukumomi da su yi duba akan lamari tare da sakin yaran su koma gaban iyayensu.

