Shugaban ƴan sandan na Kasa Kayode Egbetokun ya bayyana cewa suma da wasu yara shida daga cikin yaran da aka gurfanar da su a gaban kotu Jiya Juma’a wani shiri ne da aka shirya domin jawo hankulan mutane akan hakan da kuma batawa hukumomi su na.

Hakan na ƙunshe ne a cikin wata sanarwa da mai magana da yawun rundunar na Kasa Olumuyiwa Adejobi ya fitar a yau Asabar a shafin X a madadin shugaban ‘yan sandan.

Sanarwar ta bayyana cewa an shirya hakan ne domin jawo cece-kuce a Kasar.

Kakakin ya ce a ƙarƙashin dokokin Najeriya dukkan wanda ya kai shekarun aikata laifi, to alhakin laifi da ya yi ya rataya a wuyansa komai kankantar shekarunsa.

Acewar sanarwar zarge-zargen da ake yiwa mutanen sun haɗa da laifin lalata kayan gwamnati da yin barazana ga tsaron ƙasa da dai sauran wasu laifuka.

Sanarwar ta ce bayan faduwar yaran an gaggauta ba su tallafin magunguna, wanda hakan ya nuna jajircewar jami’an ƴan sanda na kula da walwalar yaran da ke tsare a hannunta ba tare da yin duba da zarge-zargen da suke fuskanta.

An dai gurfanar da masu zanga-zangar ne su 114 a jiya Juma’a a gaban wata babbar kotun tarayya da ke Abuja, a yayin kuma gurfanar da su, huɗu daga cikinsu da yara biyu suka suma inda aka kai su asibiti.

Bayan bayyanar lamarin ‘yan Kasar na ta Allah-wadai da irin cin zarafin da ake yiwa yaran.

Leave a Reply

%d bloggers like this: