Rundunar ‘yan sandan Jihar Bauchi ta samu nasarar hallaka wasu ‘yan bindiga shida, tare da jikkata wasu da dama a Jihar, a yayin wani sumame da ta kai karamar hukumar Ningi ta Jihar.

Kwamishinan ‘yan sandan Jihar Auwal Musa ne ya tabbatar da hakan ga manema labarai a jiya Juma’a Jihar.

Acewar jami’an bayan khallaka ‘yan ta’addan jami’an nasu sun samu nasarar kwato makami da harsasai daga hannun maharan.

Musa ya kara da cewa kafin samu nasarar jami’ansu sai da suka yi musayar wuta da maharan a kauyen Balma, Dogon Ruwa, Lambu, tsaunin Burra duk da ke cikin karamar hukumar ta Ningi a Jihar.

Kwamishinan ya ce rundunar ta na iya bakin kokarinta wajen ganin, sun kawo karshen ‘yan ta’addan a kananan hukumomin Ningi, Toro, da kuma Alkaleri a Jihar.

Leave a Reply

%d bloggers like this: