Shugaban Kasa Bola Tinubu ya bayyana cewa gwamnatinsa na sane da halin matsin da ‘yan Kasar ke ciki.

Shugaban ya ce gwamnatinsa na yin iya bakin kokarinta wajen ganin ta dauki matakin fitar da ‘yan Kasar daga cikin halin da suke ciki, tare da farfado da tattalin arzikin Kasar.

Tinubu ya bayyana hakan ne a yau Litinin a fadarsa da ke Abuja, bayan kammala rantsar da sabbin Ministoci Bakwai da yayi.

A jawabin shugaban ya ce halin matsin da Najeriya ta ke ciki a yanzu, ba iya Najeriya ba ne, harma da sauran Kasashe duniya.

Tinubu ya kuma bayyana irin ƙoƙarin da Kasar ke yi akan matsalar kalubalen tattalin arziƙin duniya, wanda ya shafi ƙasashen duniya ciki har da na Turai da Amurka.

Shugaban ya kara da cewa Annobar cutar korona ta taka muhimmiyar rawa, wajen gurgunta tattalin arzikin duniya, inda ya ce gwamnatin na yin aiki ba dare ba rana domin ganin tattalin arzikin kasar nan ya farfado daga dogon suman da yayi.

Leave a Reply

%d bloggers like this: