Gwamnan Jihar Kwara Abdurrahman Abdulrazak ya amincewa da bai’wa ma’aikatan Jihar, Alawus-alawus da ake bai’wa ma’aikata kowanne wata.

Kwamishiniyar kudi ta Jihar Hauwa Nuru ce ta tabbatar da hakan ta cikin wata sanarwa da ta fitar a shafin X na gwamnatin Jihar a yau Litinin.
Kwamishinar ta ce daga cikin wadanda za su ci gajiyar tallafin a Jihar, ciki harda ma’aikatan Kananan hukumomin Jihar.

Nuru ta ce shirin bai’wa ma’aikata tallafin kudin zai gudana na ne tsawon watanni uku daga watan Oktoba da ya gabata zuwa Disamba mai kamawa.

Nuru ta bayyana cewa bayar da tallafin zai taimaka matuka wajen rage tasirin sauyin da aka samu a harajin PAYE, wanda ake cirewa bayan samar da sabon mafi karancin albashin ma’aikatan.
Acewar Hauwa tallafin na a matsayin abin da ya dace domin tallafawa ma’aikatan, a lokacin da suke kokarin sabawa da sabon tsarin PAYE da aka samar bisa dokar harajin shiga na sirri.
A karshe Kwamishinar ta bukaci ma’aikatan Jihar da su tabbatar da ganin sun yi rajista da hukumar rajista ta jihar KWSRRA, inda ta bayyana cewa dukkan wanda bashi da rajistar ba zai samu alawus din ba.