An yi kira ga gwamnatin Jihar Kano karkashen jagorancin gwamnan Injiniya Abba Kabir Yusuf da ta bunkasa ayyukan ci gaban gamayyar hadaddiyar kungiyar fadakarwa akan sha’anin tsaro a Jihar.

Shugaban hukumar zabe mai zaman kanta ta Kano KANSIEC Farfesa Sani Lawan Malumfashi ne ya bayyana hakan, ta cikin wata sanarwa mai dauke da sa hannun mai magana da ya hukumar Bashir Habib Yahya ya fitar a yau Talata.
Malumfashi ya yi kiran ne a yayin ziyarar da Daraktan Janar na gamayyar kungiyar, fadakarwa kan sha’anin tsaro kuma tsohon kwamishinan ‘Yan sanda mai ritaya Alhaji Kabir Gwarzo ya kai masa.


Sannan shugaban na KANSIEC ya kuma yaba da irin kokarin da suke yi wajen samar da zaman lafiya da kuma bayar da gudummawarsu wajen yin zaben Kananan Hukumomin Jihar da ya gabata a wannaan shekarar ta 2024.
A karshe Lawan Malumfashi ya godewa Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso da kuma gwamnan Kano Alhaji Abba Kabir Yusuf bisa goyan baya da suke bai’wa hukumarsu ta KANSIEC.