Gwamnan Jihar Jigawa Malam Umar Namadi ya bayyana janye dakatarwar da ya yi wa kwamashinan ayyuka na musamman na Jihar Auwalu Dalladi Sankara bisa zargin da aka yi masa da kebancewa da matar aure.

Hakan na kunshe ne ta cikin wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan Ismaila Ibrahim Dutse ya fitar a yau Talata.
Sanarwar ta ce gwamna ya janye dakatarwar da ya yiwa kwamishinan nasa nan take.

Dutse ya ce gwamnan ya ɗauki matakin janye dakatarwar ne bayan da wata kotun Shari’ar Musulunci da ke nan Jihar Kano ta wanke Sankara daga zargin da ake yi masa.

A jiya Litinin ne dai Kotun shari’ar Musulunci da ke zamanta a Kofar Kudu a Kano karkashin jagorancin Alkalin Kotun mai shari’a Ibrahim Sarki Yola ya wanke kwamshinan daga zargin da ake yi masa bayan karbar rahoto daga jami’an ‘yan sanda akan lamarin.