Sanata mai wakiltar Kebbi ta tsakiya Adamu Aliero ya ce an kakkaɓe ƴan sabuwar ƙungiyar Lakurawa da su ka ɓulla a jihar.

Sanatan ya bayyana haka ne ranar Talata bayan da aka samu dauki daga ministan tsaro da babba hafsan tsaron kasa da kuma sauran jami’an tsaro.

Aliero ya ce yan kungiyar sun ketara zuwa jamhuriyar Nijar.

Sanatan ya ce sun bayyanawa ministan tsaro cewa kada a yi sakaci a kan lamarin yan Lakurawa don gudun abinda ya faru a yankin arewa maso gabas ya faru a yankin arewa maso yamma.

Ya ce yakin ana son yin shi kuma a gama cikin kwanaki biyar kacal.

Sanatan ya kara da cewa yan kungiyar sun hallaka mutane da dama a jihar Kebbi.

Sai dai lamarin ya fi shafar kananan hukumomin Argungu da Augie.

Wannan na zuwa ne baya da majalisar dattawa ta ce yan kungiyar na ci gaba da bazuwa a jihohin Kaduna, Neja, Sokoto da Kebbi.

Leave a Reply

%d bloggers like this: