Shugaban kasa Bola Tinubu ya bayyana cewa ‘yan Najeriya sun kusa darawa sakamakon wasu tsare-tsare da gwamnatinsa ke dauka domin kawo karshen matsalolin da ake fuskanta a Kasar.

Shugaban ya bayyana hakan ne a birnin Rio na Kasar Brazil a wani taro da ya halarta, ta cikin wata sanarwa da mai magana da yawunsa Bayo Onanuga ya wallafa a shafinsa na X a jiya Juma’a, shugaban ya ce tabbas ana fama da yunwa a Najeriya amma gwamnatinsa na daukar matakin kawar da yunwa da rikicin manoma da makiyaya a Kasar.
Shugaban ya ce bisa wasu shirye-shirye da gwamnatinsa ke yi akan lamarin nan bada dadewa ba za a sauki saukin tsadar rayuwar da ake fama da ita, tare kuma da samar da hanyoyin kawo bunkasa fannin noma da kiwo a Najeriya.

Shugaban na wannan kalamin ne a Kasar Barazil a lokacin da yake kulla wata yarjejeniya don inganta fannin sarrafa nama da Kamfanin JBS S.A da ke kasar ta Barazil.
