Shugaban Kasa Bola Tinubu ya nemi da majalisar dattawa da ta tabbatar da Laftanar Janar Olufemi Oluyede a matsayin babban hafsan sojin kasar.

Mai magana da yawu shugaban na musamman kan yada Labarai Bayo Onanuga ne ya bayyana hakan ta cikin wata sanarwa da ya fitar a jiya Juma’a, ya ce shugaban ya aikewa da Majalisar wasika a hukumance domin tantancewa tare da tabbatar da Olufemi a matsayin sabon babban hafsan sojin Kasar.
Sanarwar ta bayyana cewa matakin shugaba Tinubu yayi daidai da tanadin kundin tsarin mulkin Kasar nan.

Shugaban ya aikewa da majalisar wasikar ne a Jiya Juma’a, inda kuma yake neman da Majalisar ta tabbatar da Oluyede a matsayin babban hafson sojin Kasar bisa tanadib sashi na 218 (2) na kundin tsarin mulkin Najeriya na shekarar 1999 da kuma sashi na 18 (1) NA dokar sojin Kasar.

Idan ba ku manta ba dai tun a ranar 30 ga watan Oktoban shekarar shugaban Tinubu ya nada Oluyede a matsayin babban hafson sojin Kasar na riko bisa rashin lafiyar da Laftanal Janar Taoreed Lagbaja da ke kan matsayin yake fama da ita, inda kuma ya rasu a ranar 5 watan Nuwamban nan da muke ciki.