Wasu ‘yan bindiga sun hallaka akalla mutane bakwai ciki harda wani jami’in sa-kai, tare da kone buhunhunan masara 50 a garin Bangi da ke Ƙaramar Hukumar Mariga ta Jihar Neja.

Wasu majiyoyi sun shaidawa jaridar Daily Trust cewa mutanen da aka hallaka sun tafi ɗauko masara ne a gona bayan yin girbi, inda ‘yan bindigar suka mamaye m su, tare da motar da ta dauko masarar.

Bayan yi musu kwanton baunar da maharan suka yi sun hallaka duk wanda ke cikin motar, tare da kone motar da masarar ke ciki.

A lokacin da maharan suka mamaye manoman sai da suka bari, suka kammal loda buhunhunan masarar 50 a cikin motar, inda su na barin gonar suka bude musu wuta suka hallaka mutanen daga bisani suka bankawa motar wuta.

Manoma a karamar hukumar ta Mariga na fuskantar kalubale a yayin girbe amfanin gonarsu, bisa kai hare-hare, da kashe-kashe da kuma garkuwa da mutane da ’yan bindiga ke yi a cikin yankin.

A wani labarin kuma ’’yan ta’addan sun hallaka wani mazaunin garin Kontagora mai suna Malam Danjuma bayan karbar kuɗin fansa Naira miliyan 20 daga hannun iyalansa, bayan shafi makwanni uku a hannunsu.

Mai magana da yawun rundunar ’yan sandan Jihar ta Neja, SP Wasiu Abiodun, ya tabbatar da hallaka manoman.

Kakakin ya ce a ranar 16 ga watan Nuwamban nan da misalin ƙarfe 3 na rana, maharan suka yiwa manoman kwaton ɓauna, wanda hakan ya yi sanadiyyar mutuwar wasu daga cikinsu.

Kakakin ya ce tuni aka aike da hadin gwiwar jami’an tsaro na ‘yan sanda da sojoji yankin domin dakile ‘yan ta’addan.

 

 

 

Leave a Reply

%d bloggers like this: