Hukumar yaki da masu yi wa tattalin arzikin ƙasa zagon kasa EFCC ta gurfanar da tsohon gwamnan jihar Kogi Yahaya Bello a gaban kotu.

Hukumar ta gurfanar da Yahaya Bello yau a gaban babbar kotun tarayya da ke Maitama a Abuja.
An gurfanar da shi ne bayan zargin almundahanar sama da naira biliyan 80 lokacin ya na gwamna a jihar
Hukumar ta kama Yahaya Bello jiya Talata bayan da ya ziyarci ofishin.

Tun a watan Afrilu hukumar ke nemansa ruwa a jallo bayan aike masa da takardar gayyata daban-daban har daga bisani ta ayyanashi a matsayin wanda take nema ruwa a jallo.

Wasu rahotanni sun ce an kama Yahaya Bello ne bayan samun bayanai a kansa.
Bayanan sun ce ba kansa ya kai bisa ra’ayinsa ba.
Daga karshe dai hukumar ta gurfanar da shi a gaban mai shari’a Justice Maryanne Anenih da ke Maitama a Abuja.