Rundunar sojin saman Najeriya ta samu nasarar hallaka fiye da yan bindiga 20 tare da lalata makamansu
Hakan ya faru bayan hare-haren da su ka kai guda biyu a ranar 25 ga watan Nuwamba da mu ke ciki.

An kai harin yankin Kukawa sa ke jihar Borno bayan da jami’an ƙarƙashin Operation Hadin Kai su ka kai harin.
Hakan na kunshe a wata sanarwar da mai magana da yawun sojin Air Commodore Olusola Akinboyewa ya fitar.
Ya ce sun lalata wata motar yaƙi ta mayaƙan.

Ya ƙara da cewa bayan harin da su ka kai a kan motar yaƙin, sun samu kiran gaggawa cewar yan bindiga sun kai hari haye kan babura.

Ya ce sun yi gaggawar kai ɗauki tare da kashe wasu da sama yayin da wasu su ka bar baburansu sama da 20.
A cewarsa, sun gudu ɗauke da raunin harbin bindiga a jikinsu.
Ya ce rundunar za ta ci gaba da aikin tabbatar da tsaro a ƙasar.