Gwamnatin tarayyar Najeriya ta ce ƙasar na asarar sama da dala biliyan ɗaya sakamakon zazzaɓin cizon sauro.

Ministan Lafiya a Najeriya Farfesa Ali Pate ne ya bayyana haka ya ce ana yin asarar ne kowacce shekara.

A cewarsa hakan ya fito ne bayan da aka fitar da kididdigar kuɗaɗen da ake asara a bangaren.

Ya ce zazzabin cizon sauro ba iya cuta ce da ke illata jiki kaɗai ba, har da tattalin arziki.

A sakamakon haka ya buƙaci a kawo daukin gaggawa.

Ya ce a shekarar 2022 aama da yara 180,000 yan kasa da shekara biyar ne su ka mutu sakamakon zazzaɓin cizon sauro.

Ministan ya kada wani kwamitin karbar shawarwari da tsare-tsare don ganin an daƙile cutar da ke illata lafiya da tattalin arzikin ƙasa.

Leave a Reply

%d bloggers like this: