Shugaban kasa Bola Tinubu ya nada Jami’u Abiola da ga MKO Abiola a matsayin hadimi na musamman a bangaren yarurruka da harkokin kasashen ketare.

Sakataren Gwamnatin Tarayya Sanata George Akume ne ya bayyana hakan a yau Laraba, ta cikin wata sanarwa.

Sanarwar ta bayyana cewa mukamin da shugaban ya nada Jami’u Abiola ya fara aiki ne tun daga ranar 14 ga watan Nuwamban nan da muke ciki.

Kafin shugaba Tinubu ya nada Jami’u a matsayin mai kula da yararruka, ya taba rike mukamin hadimi a bangaren ayyuka na musamman a ofishin mataimakin shugaban kasa.

Bayan nadin Shugaba Tinubu ya bukace shi da ya hadaka kai da ma’aikatar harkokin kasashen waje, da kuma kwarewarsa gurin samar da sauye-sauye a kasar.

Leave a Reply

%d bloggers like this: