Gwamnatin Jihar Osun karkashin jagorancin gwamna Ademola Adeleke ta sanya naira 75,000 a matsayin sabon mafi karancin albashi ga Ma’aikatan Jihar.

Gwamnatin ta ce sabon mafi karancin albashin zai fara aiki ne daga ranar 1 ga watan Disamba mai kamawa, inda kuma za ta hade musu da bayin da suke bin ta na wata guda, idan aka fara biyan sabon albashin.

Hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da gwamnatin Jihar ta Osun ta wallafa a shafinta na X a yau Juma’a, inda ta bayyana cewa daukar matakin fara biyan ma’aikatan Jihar sama da naira 70,000 din ne a wani taro taro da ta gudanar bisa jagorancin mataimakin gwamnan Jihar Kola Adewusi.

Sanarwar ta ce hakan wani bangare ne da gwamnatin Jihar ta dauka na tabbatar da walwala da jindadin ma’aikatan Jihar.

Sanarwar ta bayyana cewa taron da aka gudanar ya samu halartar ‘yan kungiyar kwadago, kuma jami’an gwamnatin Jihar.

Leave a Reply

%d bloggers like this: