Babbar kotun tarayya da ke birnin tarayya Abuja ta dage zamanta na yau Juma’a a sauraron karar da hukumar yaki da masu yiwa tattalin arzikin kasa zagon Kasa ta EFCC ta shigar da tsohon gwamnan Jihar Kogi Yahya Bello gabanta kan zarginsa da ta ke yi masa na yin sama da fadi da sama da naira biliyan 80 a lokacin da yana kan kujerar gwamnan Jihar.

Kotun karkashin alkalin ta mai shari’a Emeka Nwite ta dage ci gaba da sauraron karar ne bisa gaza bayyanar lauyoyin Yahya Bello zaman kotun na yau.
Koda a jiya Alhamis sai da hukumar ta EFCC ta gabatar da Yahya Bello a kotu kan sabbin zarge-zarge 19 da take yi masa kan aikata badakala.

Bayan gaza halartar lauyoyin Yahya Bello a gaban kotun, lauyan hukumar ta EFCC Kemi Pinheiro SAN ya bukaci da kotun, ta bayar Yahya Bello yayi bayani da kansa, sakamakon doka ta bayar da damar wanda ake kara matukar ya bayyana a gaban kotu zai iya kare kansa ko da babu lauyoyinsa.

A yayin da aka tambayi Yahya Bello rashin halartar lauyoyinsa zaman, ya ce bai samu labarin zaman ba, sai a cikin daren jiya Alhamsi, inda kuma yake kyautata zaton lauyoyin nasa ba su samu labarin zaman ba, duba da cewar an dage karar zuwa ranar 21 ga watan Janairun shaekarar 2025 mai kamawa.
Sai dai Alkalin bai amshi rokon lauyan na EFCC ba, sakamakon bai bai’wa Yahya Bello damar yin bayani da kansa ba, sai dai Alkalin ya bayar da umarnin sanar da lauyoyin Tsohon gwamnan na kogi, zama na gaba a ranar 13 ga watan Disamba mai kamawa.
A ranar larabar da ta gabata ne dai EFCC ta gurfanar da Yahya Bello a gaban kotun bayan da ya mika kansa gabanta a ranar Talata, bayan shafe tsawon lokaci ta na farautarsa.