Akalla mutane sama da 200 ne hadarin jirgin kwale-kwale ya rutsa da su a wani kogi da ke yankin Bambo-Ebuchi a Jihar Neja.

Lamarin faru ne a yau Juma’a, inda ake kyautata zaton mutane da dama sun rasa rayukansu.
Shaidun gani da ido sun bayyana cewa jirgin wanda ya kasance mallakin wani mutum ne mai suna Musa Dangana ya dauko fasinjoji akalla fiye da 200, inda za su tafi cin Kasuwa.

Jirgin kwale-kwalen wanda ke dauke da mata masu cin kasuwa, da manoma inda za su tafi kasuwar da ke ci kowanne mako a Katcha.

Shaidun sun bayyana cewa ana kyautata zaton cewa mafiya yawa daga cikin wadanda ke cikin Kwale-kwale sun mutu, inda jami’an bayar da agajin gaggawa suka dauko gawarwakin mutane Takwas, yayin da suke ci gaba da aikin ceton ragowar.