Kungiyar kasuwanci ta Duniya WTO ta sake zabar tsohuwar ministar kudi ta Najeriya Ngozi Okojo-Iweala a matsayin shugaban kungiyar a karo na biyu.

Iweala za ta ci gaba da shugabantar kungiyar ne tsawon shekaru hudu.
A sanarwar da shafin kungiyar na X ya fitar a yau Juma’a, ya bayyana cewa sabon nadin Ngozi zai fara aiki a ranar 1 ga watan Satumban shekarar 2025 mai kamawa.

Shugaban Majalisar gudanarwar kungiyar Ambasado Petter Olbery na Kasar Norway, ya bayyanawa ‘yan kungiyar cewa babu wani wanda ya nemi yin takara da Iweala kafin karewar wa’adin ranar 8 ga watan Nuwamban nan ya ciki.

Shugaban ya ce an sake nada Okonjo-Iweala ne bisa amincewa da shugancinta, da kuma amincewar Kasashe 166 da ke cikin kungiyar ta WTO.
Ngozi Okonjo-Iweala wadda ta kasar ‘yar Najeriya ce, itace mace ta farko ‘yar afrika da ta fara rike shugabancin kungiyar, tun a ranar 1 ga watan Maris din shekarar 2021 da ta gabata.