Hukumar karfar korafe-korafen jama’a da yaki da cin hanci da rashawa ta Jihar Kano PCACC ta yi amai ta lashe akan batun da ta yi na cewa ta kama buhunhunan shinkafa 16,800 wadda ake kyautata zaton shinkafar tallafin da gwamnatin tarayya ce ta bai’wa Jihar.

Shugaban hukumar Muhyi Magaji Rimin-Gado ya bayyana asalin mamallakin shinkafar da aka yi zargin cewa an karkatar da ita tun da farko.

Barista Muhyi Rimin-Gado ya tabbatar da cewa an kawo Shinkafar Jihar Kano ne daga Jihohin Bauchi da Zamfara, amma ba tallafin da shugaba Bola Tinubu ne ya bai’wa Jihar.

Shugaban ya kara da cewa Shinkafar ta wani mutum ce da ke tallafawa marasa karfi, don fitar da su daga cikin halin kuncin rayuwa.

A makon nan ne dai hukumar ta fito ta bayyana cewa ta kama shinkafar tallafin gwamnatin tarayya mai dauke da hutuna nan shugaba Bola Tinubu ana canza mata buhu a wani guri a nan Jihar Kano.

 

Leave a Reply

%d bloggers like this: