Jami’ab rubdubar sojin Najeriya na sashi na biyu a rundunar Opration Hadin kai, tare da jami’an sa-kai a Jihar Yobe sun dakile wani hari da ‘yan boko haram suka yi yunkurin a Jihar.

Hadin gwiwar jami’an sun samu nasarar dakile harin ne a Kauyen Fegi da ke yankin Buni Yadi a cikin karamar hukumar Gujba ta Jihar.

Jami’an sun kuma samu nasarar hallaka wani kwamadan ‘yan ta’addan a yankin mai suna Abu Shekau da wasu mabiyan hudu.

Mai sharhi kan sha’anin tsaro a yankin tafkin Chadi, Zagazola Makama ne ya tabbatar da hakan a jiya juma’a a wata wallafa da yayi a shafinsa na X.

Makama ya bayyana cewa ‘yan ta’addan sun nufi kai harin ne da karfe 11 na safiya, inda hadin gwiwar Jami’an suka fatattake su da musayar wuta.

A yayin musayar wutar Jami’an sojin sun kwato makamai daga hannun ‘yan ta’adda a lokacin da suke gudun tsira da ransu.

Leave a Reply

%d bloggers like this: