Gwamnan Jihar Katsina Malam Umar Dikko Radda ya tabbatar da naira 70,000 a matsayin sabon mafi karancin albashin ma’aikatan Jihar.

Gwamnan ya tabbatar da hakan ne ta cikin wata wallafa da yayi a shafinsa na X a safiyar yau Asabar.

Gwamna Radda ya ce ya amince da naira 70,000 din ne a matsayin mafi karancin albashin bayan kammala tattaunawa da aka yi akansa.

Radda ya kara cewa Ma’aikatan Jihar za su fara samun sabon albashin ne a watan Disamba mai kamawa.

Acewarsa karin zai shafi dukkan wani ma’aikaci a kowanne mataki na Jihar, da Kananan Hukumomi da kuma hukumar da ke kula da ilmi ta kananan hukumomin Jihar.

Sannan gwamna Radda ya kuma mika godiyarsa ga ma’aikatan Jihar bisa hakurin da suka yi, har aka kawo wannan matakin.

 

Leave a Reply

%d bloggers like this: