Gwamnan Jihar Edo Sanata Monday ya bayar da umarnin biyan ma’aikatan Jihar karin Albashin na watanni 13.

Shugaban Ma’aikatan Jihar Anthony Okungbowa ne ya tabbar da hakan a jiya Juma’a, inda ya ce gwamnan ya kuma sake bayar da umarnin daukar dalibai ‘yan asalin da suka kammala karatun digiri da sakamako mafi kyau daga kowacce Jami’a a Najeriya ko a Ketere, da a dauke su aiki kai tsaye.
Shugaban Ma’aikatan ya ce shirin daukar daliban aiki a Jihar , an bijiro da shi ne domin da ganin an dauki nagartattun Ma’aikata aiki.

Shugaban ya kara da cewa gwamnan ya yi hakan ne domin karfafa gwiwar ma’aikatan Jihar don ganin sun ci gaba da gudanar da ayyukansu yadda ya kamata.
