Wani mai maganin gargajiya mai suna Ismail Usman ya harbi kansa a lokacin da yake gwajin maganin bindiga a yankin Kuchibiyi da ke Karamar Hukumar Bwari a birnin Abuja.

Wani mazaunin Kuchibiyi Samson Ayuba ya ce lamarin ya faru ne a ranar Alhamis, a lokacin da mutumin ya ke kokarin gada ingancin maganin bindgar da ya hada.

Ya ce sai dai bayan faruwar lamarin an yi gaggawar kai shi asibitin gwamnati da ke Kubwa bayan ya fadi, inda kuma ya samu raunuka.

Mai magana da yawun rundunar ‘yan sandan birnin na Abuja Joesephine Adeh ta tabbatar da faruwar lamarin ta cikin wata sanarwa da ta fitar.

Adeh ta ce sun samu rahotan cewa wani mai maganin gargajiya ya harbe kansa a lokacin da yake gwajin maganin bindigar da ya hada.

Sai dai ta ce sakamakon munanan raunukan da ya samu aka kai shi asibitin Kubwa domin duba lafiyarsa, daga bisani kuma aka mayar da shi asibitin kwararru da ke Gwagwalada domin kara samun kulawa.

Kakakin ta kara da cewa abinciken da aka gudanar a gidansa an gano wata bindigar gargajiya da layu wadanda ya yi amfani da su gurin gwajin maganin bindigar.

Adeh ta ce a halin yanzu su na ci gaba da gudanar da bincike kuma za su gurfanar da shi a gaban kotu bisa zarginsa da mallakar makami ba bisa ka’ida ba tare da yunkurin hallaka kansa.

 

Leave a Reply

%d bloggers like this: