Mataimakin shugaban Majalisar Dattawa Sanata Barau I Jibril ya bayyana damuwarsa kan yadda al’ummar Kasar nan suka gaza fahimtar sabon kudin karin haraji a Kasar.

Barau ya bayyana hakan ne ta cikin wata sakon murya da ya wallafa a shafinsa na Facebook a yau Asabar.

Barau ya ce bai kama mutane su dinga yin Allah-Wadai da hakan ba, duba da cewa ba su gama fahimtar kudurin ba.

A sakon muryar da Barau ya wallafa ya bayyana wayar da kan al’umma akan kudurin harajin da ya tsallake karatu na farko, inda ya ce tsallake karatu na biyu da kudurin ya yi ba hakan ne ya ke nuna cewa an kammala ba, inda ya ce yanzu ma aka fara zama akansa.

Acewar Sanatan kafin fara zama akan sabon kudurin sai da suka tattauna da masan, don yi musu bayani akai, duba da cewa akwai wadanda ba su san mai kudurin ke dauke da shi ba.

Barau ya ce a yanzu ne Majalisar ta fara zama akan batun tare da yin muhawara akansa.

Sanata Barau na wannan Kalami ne, bayan da al’ummar Kasar nan ke yin Allah-Wadai da sabon kudurin dokar harajin da shugaba Bola Tinubu ya aikewa da Majalisar ta Dattawa kudurin, tare da sukar Sanatocin Arewa Muhamman Mataikamin shugaban Majalisar Barau Ibril wanda ya jagoranci zaman Majalisar a ranar Larabar da ta gabata.

Leave a Reply

%d bloggers like this: