Tsohon mataimakin shugaban kasa Alhaji Atiku Abubakar ya bayyana cewa dan takarar shugaban Kasa a jam’iyyar Labour Party Peter Obi ya kai masa ziyara gidansa da ke Jihar Adamawa.

A wani faifan bidiyo da Alhaji Atiku ya fitar, ya ce Peter ya kai masa ziyarar ne a yau Asabar.
Sai dai Alhaji Atiku bai bayyana dalilin ziyarar da Peter Obi ya kai masa ba, da kuma abinda suka tattauna.

Rahotannin sun bayyana cewa ziyarar da Peter Obi ya kai’wa Atiku ba ta rasa da batun cimma matsaya a hadewarsu a zaben 2027 mai zuwa.
