Shugaban Jam’iyyar APC na Kasa Dr Abdullahi Umar Ganduje tare da Sarkin Kano na 15 Alhaji Aminu Ado Bayero sun jagoranci bude sabon Masallacin Juma’a da Makarantar Islamiyya a Karamar hukumar Takai a Kano a jiya Juma’a.

Hadimin Ganduje a bangaren kafafan sada zumunta Salihu Tanko Yakasai ne ya bayyana hakan ta cikin wata sanarwa da wallafa ashafinsa na Facebook a jiya Juma’a.

Sanarwar ta bayyana cewa Gidauniyar Ganduje Foundation ce ta daukin nauyin ginin Masallacin da Makarantar, a Unguwar Gidan Goje da ke Karamar hukumar ta Takai a Kano.

Salihu ya kara da cewa Dr Ganduje da Aminu Ado sun kuma tabbatar da musuluntar da Maguzawa akalla 400 a cikin Karamar hukumar.

Sanarwar ta ce a yayin bude Masallacin ya samu halartar Wakilin shugaban darikar Kadiriyya na Afrika Sheikh Dr Kariballah Sheikh Dr Muhammad Nasir Kabara, da shugaban hukumar aikij hajji na Kasa NAHCON Sheikh Abdullah Saleh Pakistan, da Shugaban Kungiyar Izala ta Kasa Sheikh Abdullahi Bala Lau, da Sakataren Kungiyar Sheikh Kabiru Gombe, da kuma sauran Malamai daban-daban da suka halarci taron.

Leave a Reply

%d bloggers like this: