Gwamnan babban bankin Kasa na CBN Olayemi Cardoso ya gargadi bankuna kan take doka da kuma boye takardun kudi a Kasar.

Cardoso ya gargadi bankuna ne a gurin wata liyafa da CIBN ta shirya a Jihar Legas a jiya Juma’a.

Gwamnan bankin ya bayyana cewa daga gobe 1 ga watan Disamba, jami’an babban bankin Kasa za su fara yawo domin duba na’urorin cirar kudi na ATM na bankunan Kasar.

Olayemi Cardoso ya kara da cewa dukkan bankin da suka kama da aikata laifin boye takardun kudin, da kin zubawa a na’urar ATM zai fuskanci hukunci daidai da abin da ya aikata.

Gwamna Babban bankin na CBN, ya ce bankin na CBN zai ci gaba da sanya idanu akan harkokin hada-hadar kudi ,domin samar da wadatattun takardun kudi ga ‘yan Najeriya musamman saboda karshen shekarar 2024.

Hakan dai na zuwa ne a daidai lokacin da aka fara samun Karancin takardun kudi a hannun al’umma, wanda hakan ya sanya masu na’urar POS suka fara karin kudin caji ga masu cirar kudi a gurinsu.

 

Leave a Reply

%d bloggers like this: