Shugaban Jam’iyyar APC na Kasa Dr Abdullahi Umar Ganduje, ya sha alwashin cewa Jam’iyyarsu ta APC za ta kwace mulkin Jihar Rivers daga hannun Jam’iyya mai mulki ta PDP a yayin zaben shekarar 2027 mai zuwa.

Ganduje ya bayyana hakan ne a ranar Asabar a gurin taron rantsar da sabbin shugabannin jam’iyyar APC na Jihar.

Shugaban jam’iyyar ya rantsar da Chif Tony Okocha da karin wasu mutane 22 a matsayin shugabannin jam’iyyar, bayan zabensu da aka yi a taron jam’iyyar na Jihar wanda aka gudanar makwanni biyu da suka gabata a garin Fatakwal dake Jihar ta Rivers.

A yayin taron shugaban jam’iyyar na Kasa ya samu rakiyar sauran mambobin Kwamitin Zartarwa na Kasa 16, inda ya bukaci da mambobin jam’iyyar ta APC da su goyi bayan sabbin shugabannin Jihar, don tabbatar da nasarar jam’iyyar ta su a zaben shekarar 2027.

Dr Abdullahi Umar ya bayyana cewa nasarorin da Jam’iyyarsu ta APC ta samu a yankin Kudu maso Kudu, wanda a baya ake ganin yankin PDP ne, yana mai nuni da nasarar da jam’iyyar APC ta samu a Jihohin Cross River da kuma Edo.

Acewarsa a halin yanzu jam’iyyar APC ta Kasa Jihar Rivers ta sanya a gaba a zaben shekarar 2027.

 

Leave a Reply

%d bloggers like this: