Gwamnan Jihar Kaduna Sanata Uba Sani ya nada bai bashi shawara kan harkokin Kananan hukumomin Jihar.

Gwamnan ya nada Kabiru Yakubu Jarimi ne a matsayin wanda ya kasance tsohon shugaban Karamar hukumar Kaduna ta Kudu a Jihar.

A wata sanarwa da babban sakataren yada labaran gwamnan Ibraheem Musa ya fitar a yau Asabar, ya ce nadin zai fara aiki ne nan take.

Sanarwar ta bayyana cewa ana sanya ran Kabiru zai yi aiki da gogewar da yake da ita a harkokin kananan hukumomi, domin ganin ya samu nasarar da ake bukata.

Sannan gwamnan ya bukace shi da ya yi kokarin ganin ya sauke nauyin da aka dora masa ta hanyar sadaukarwa Adalci da kuma jajircewa a cikin aikinsa.

Leave a Reply

%d bloggers like this: