Gwamnatin tarayya ta kaddamar da shirin bayar da tallafin kayan noman alkama domin kara bunkasa harkokin noman a Kasar da kuma rage dogaro da shigo da kayan abinci daga kasashen wajen.

Ma’aikatar yada labarai ce ta bayyana hakan, ta cikin wata sanarwa, inda ta ce Ministan Kudi Wale Edun ne ya tabbatar da hakan a lokacin da ya ke ganawa da manema labarai a birnin tarayya Abuja.

Edun ya ce shirin zai taimaka wajen bunkasar tattalin arzikin karkara da kuma rage dogara da shigo da Alkama Kasar nan, da kuma samun babbar nasara wajen samar da wadatacceb abinci a Najeriya.

Isyaku Buba daraktan shirin ya bayyana cewa gwamnatin za ta tallafawa manoma 280,000, inda kuma kananun manoma daga Jihohi 16 na Kasar nan ne za su ci gajiyar shirin.

Acewarsa za kuma a bai’wa manoman tallafi, da ya kai kashi 25 cikin 100 na irin Alkamar, da kuma kashi 50 cikin 100 na takin zamani don saukakawa manoman farashin.

Buba ya kara da cewa, an kafa cibiyoyin bayar da tallafin 409, daga cikin su 281 sun fara aiki a halin yanzu, inda ake sanya ran manoma 68,389 za su amfana.

Har ila yau ya ce ana sanya ran za a kammala shirin bayar da tallafin a Karshen watan nan na Disamba, wanda hakan yayi daidai da lokacin noman na Alkama.

Sannan ya ce an samar da jami’an tsaro a dukkan guraren bayar da tallafin.

Leave a Reply

%d bloggers like this: