Shugaban Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa INEC Farfesa Mahmood Yakubu, ya musanta rahotannin da ake yaɗawa cewa ya rigamu gidan gaskiya.

Mahmud ya bayyana hakan ne a yau Asabar, a cikin wata sanarwa da hadiminsa na musamman kan yaɗa labarai Mista Rotimi Oyekanmi ya fitar.

Rotimi ya ce ko kadan babu kamshin gaskiya a cikin rahotannin da ake yadawa na rasuwar shugaban na INEC a birnin Landan.

Acewarsa sun samu batun ne a shafukan sada zumunta, inda ya ce an fara yada hakan ne tun a ranar 9 ga watan nan na Disamba.

Rotimi Oyekanmi Farfesa Yakubu yana nan cikin ƙoshin lafiya, inda ya ce bai Farfesan bai je Landan ba cikin shekaru biyu da suka gabata ba.

Sannan ya ja hankula mutane da su kaucewa yada irin wannaan jita-jitar da ba ta kamata ba.

Shugaban hukumar zaben ya musanta batun ne bayan bullar wata jita-jita da ke nuni da cewa ya rasu bayan fama da gajeriyar rashin lafiya a wani Asibiti da ke birnin Landan.

Leave a Reply

%d bloggers like this: