Majalisar dokokin Kasar Koriya ta Kudu ta tsige shugaban Kasar Yoon Suk-Yeol bisa bayyana dokar mulki sojin da ya sanya a Kasar wadda kuma ta haifar da bore a ƙasar.

Majalisar ta tsige shi ne bayan kada kuri’ar amincewa da tsige shi, inda ‘yan majalisa 204 suka goyi bayan kudirin a zaman majalisar da aka gudanar a yau Asabar, ya yin da wasu 85 ba su amince ba, inda uku wasu daga cikin su suka ki jefa kuri’a, yayin da kuma aka soke kuri’u takwas.
Sai dai bayan kalamam shugaban kasar al’ummar Kasar na ta yin kiraye-kirayen ya sauka daga shugabancin Kasar, inda yayi watsi da kiraye-kirayen, wanda hakan ya sanya Majalisar ta dauki matakin tsige shi daga shugabancin Kasar.

Bayan ayyana tsige shi da Majalisar ta yi mai mambobi 300 Al’ummar kasar sun fara gudanar da murnar tsige shi.

Bayan tsige shi hakan na nufin Yoon zai gaggata fita daga ofishinsa, inda firaminista Kasar zai ci gaba da jagorantar Kasar a matsayin shugaban riko.