Gwamnan Jihar Borno Babagana Umara Zulum ya bayar da umarnin fara biyan ma’aikatan Jihar Albashin watan Disamban da muke ciki.

Gwamnan ya ce bai’wa ma’aikatan albashin hakan zai taimaka musu wajen gudanar da bukukuwan kiristimeti da na sabuwar shekara.
Mai magana da yawun gwamnan Dauda Ilya ne ya bayyana hakan ta cikin wata sanarwa da ya fitar a yau Asabar.

Ilya ya ce gwamnan ya bayar da umarnin fara biyan ma’aikatan albashin watan na Disamba ne a jiya Juma’a.

Sanarwar ta ce hakan zai taimakawa mabiya addinin kirista, da sauran mabiya wasu addinan don ganin sun shirya bukukuwan karshen shekara cikin kwanciyar hankali.
Dauda Ilya ya kara da cewa tuni aka cika umarnin gwamnan na fara biyan ma’aikatan, inda kuma gwamnan ya bukaci ma’aikatan da su yiwa Jihar addu’o’in zaman lafiya dama Kasar baki daya.