Tsohon shugaban Majalisar wakilai Yakubu Dogara ya yaba da salon yadda shugaban Kasa Bola Tinubu ke tafiyar da salon mulkinsa.

Acewar Dogara yana goyan bayan dukkan tsare-tsaren Tinubu da ya kaddamar duba da cewa su suka fi dacewa da Kasar.

Tsohon shugaban Majalisar ya bayyanaa hakan ne a Jihar Ondo, a gurin bikin yaye dalibai karo na 14 na Jami’ar Achievers da ke Owo a Jihar.

Dogara ya kara da cewa shugaba Tinubu hazikin mutum ne duba da yadda yake jan ragamar kasar cikin iya tafiyar da mulki ydda ake bukata.

Dogara ya ce rashin jarumin shugaba da Najeriya ta gaza samu ne ya jefa Kasar cikin damuwa, na rashin ci gaba da kuma fannin tattalin arziki.

Acewarsa Dogara ya na goyan bayan dukkan yadda Tinubu ke jagorantar kasar nan.

 

Leave a Reply

%d bloggers like this: