Kamfanin rarraba hasken wutar Lantarki a Birnin tarayya Abuja ya bayyana cewa za a samu rashin wutar lantarki na kimanin mako biyu a wasu daga cikin sassan birnin daga ranar Litinin mai zuwa.

A wata sanarwa da kamfanin ya fitar a jiya Juma’a, ya ce za a samu katsewar wutar ne sakamakon gyaran da zai gudanar tare da rage nauyin daga wasu tashishi da ke ba da wuta na Migawatte 33 da kuma na megawatt 132 na Kukwaba zuwa Apo a birnin.

Kamfanin ya bayyana cewa daga cikin unguwannin da rashin wutar zai shafa sun hadar da Lugbe, kan titin zuwa Airport, Kapwa, NNPC, Games Village da kuma babban filin wasa na Kasa na Mashood Abiola wato National Stadium.

Sauran su ne Bwari yankin Kubwa, Gudu,Gbazango, Jahi, Jabi, Karu da wasu sassan birnin da kuma Keffi da ke Jihar Nasarawa.

Leave a Reply

%d bloggers like this: