Hukumar hana fasa kauri ta Kasa Kwastam ta ce akalla mutane 573,519 ne suka nemi guraben aiki a Hukumar.

Hukumar dai ta fitar da sanarwar neman daukar jami’ai 3,927 daga watan Disamba 2024 zuwa watan Fabrairun 2025 da muke ciki.
Mai magana da yawun hukumar Abdullahi Maiwada ne ya tabbatar da cewa tun bayan dube gurbin neman aiki da hukumar ta yi, ya zuwa yanzu mutane 573,519 ne suka cike fom din neman aikin da hukumar ta fitar.

Maiwada ya bayyana cewa akwai rukuni na mutane biyu da suka nemi aikin a bangaren ma’aikata masu mataimawa inda ya ce Kwararru ne, sai kuma jami’an ayyuka na gama gari.

Har ila yau Abdullahi Maiwada ya kara da cewa akwai kuma mutane 249,218 da suka nemi aikin a karkashin matakin sufuritanda na ayyukan gama gari.
Kakakin Hukumar ya kara da cewa a matakin sufuritanda jami’ai masu tallafawa, akwai mutane 27,722 da suka nemi gurbin aiki tare da gabatar da takardunsu na HND da kuma digiri.
Sai kuma matakin sufeto mutane 115, 634 nemi suka nemi aikin a bangaren gama gari, sa kuma mutane 12,952 kuma a bangaren jami’ai masu taimakawa, inda suka nema ta hanyar takardunsu na NCE wasu dana ND wato Diploma.
Jami’in ya kara da cewa akwai wadanda suka nemi aikin da takardunsu na Sakandire.
Abdullahi ya ce yawan mutanen da suka nemi aiki a hukumar hakan ya nuna cewa aka masu son shiga aikin hukumar, inda ya ce a halin yanzu hukumar na ci gaba da tantance masu neman aikin, don zabar wadanda suka cancanta.
A makon da ya gabata ne dai Ministan Kudi Wale Edun ya ce gwamnatin Tarayya ta amince da daukar Ma’aikata 3,927 a hukumar ta Kwastam.