Gwamnan jihar Borno Babaga Zulum.ya yi ala wadai a harin da mayakan ISWAP su ka kai wa jami’an soji a jihar

An kai harin a ranar 4 ga watan Janairu da mu ke ciki.
Kwamishinan yaɗa labarai a jihar Farfesa Usman Tar ya bayyana haka a wata sanarwa mai dauke da sa hannusa.

Gwamnan ya ce harin da mayakan su ka kai yunkuri ne ka kawo cikas da koma baya a cigaban da ake samu a bangaren tsaro a jihar.

Sannan ya mika sakon taaziyyarsa ga iyalan wadanda su ka rasa rayukansu.
Gwamna Zulum kuma yabawa jami’an tare da karfafarsu domin ci gaba a ayyukan da su ke yi.
Haka kuma ya ce gwamnatinsa za ta ci gaba da aiki da jami’an sojin don ganin an ci gaba da samun zaman lafiya da cigaba a jihar.
An kai wa jami’an sojin hari ne a sansaninsu da ke Sabon Gari a karamar hukumar Damboa a jihar ranar 4 ga watan Janairu.
Sannan aka cinnawa sansanin wuta da kuma motocin jami’an.
Sai dai jami’an sun dakile harin tare da halaka sama da mayakan 30 bayan da su ka samu ɗauki daga jami’an sojin sama.