Babban sufeton yan sandan Najeriya Kayode Egbetokun ya buƙaci da a gaggauta ɗaukar mataki kan harin da mayakan Boko Haram su ka kai wa jami’an a jihar Borno.

Hakan na kunshe a wata sanarwa da mai magana da yawun yan sandan Najeriya Muyiwa Adejobi ya fitar a yau Juma’a.

A cewarsa an hallak jami’an su biyu da su ka haɗa da Isfekta Bartholomew Kalawa da Kofur Mustapha Huzaifa.

Babban sufeton yan sandan na ƙasa ya buƙaci mataimakinsa da ke shiyya ta 15 da ya gaggauta aike da karin jami’ai domin ɗaukar mataki.

Sufeton ya ce ya zama wajibi a kama wadanda su ka hallaka jami’an domin hukuntasu, a cewarsa lamarin ba zai tafi ba tare da an hukuntasu ba.

Tuni Kwamishinan yan sanda a jihar ya ziyarci wajen da lamarin ya faru tare yabawa jami’an da su ka jajirce wajen dakike harin.

Leave a Reply

%d bloggers like this: