A gobe Asabar ne shugaban Kasa Bola Tinubu zai bar birnin tarayya Abuja zuwa Kasar Dubai, domin halartar dorewar tattalin arzikin Duniya na shekarar 2025 da muke ciki wato (ADSW 2025).

Bayo Onanuga mai magana da yawun ne ya tabbatar da hakan ta cikin wata sanarwa da ya fitar a yau Juma’a.
Sanarwar ta bayyana cewa shugaban zai tafi Hadaddiyar Daular laraban ne, bayan shugaban Kasar ta Dubai Sheikh Mohamed bin Zayed Al Nahyan ya gayyace shi taron wanda za a gudanar a ranar 12 zuwa 18 ga watan Janairu nan.

Bayo ya bayyana cewa taron zai samu halartar manyan shugabannin duniya, masana, ‘yan kasuwa, masu ruwa da tsaki, da kuma kungiyoyin fararen hula.

Sanarwar ta kara da cewa a yayin taro za a tattauna akan irin nasarorin da aka samu a bangaren tattalin arziki zamantakewa, tare da samar da hanyar da za a ci gaban da aka samun nasarori.

Onanuga ya kara da cewa a yayin taron Shugaba Tinubu zai kara jaddada gudurorin gwamnatinsa na makamashi, sufuri, lafiya, da kuma ci gaban tattalin arziki.

Acewarsa shugaban zai kuma yi wata ganawa da fadar sarkin Kasar don tattaunawa akan al’amuran da suka shafi Kasashen biyu.

Ministan harkokin wajen Najeriya Ambassador Yusuf Tuggar na daya daga cikin wadanda za su raka shugaba Tinubu taron.

A karshe sanarwa ta ce ana sanya ran shugaban Tinubu zai dawo gida Najeriya bayan kammala taron a ranar 16 ga watan Janairun.

 

Leave a Reply

%d bloggers like this: