Hukumar Yaki da masu yiwa Tattalin Arzikin Ƙasa zagon Kasa ta EFCC ta kama wasu mutane 105 ciki harda ’yan Kasar China huɗu da ake zarginsu da aikata damfara ta kafar Internet a Abuja.

Mai magana da yawun hukumar Dele Oyewale ne ya tabbatar da kama mutane ta cikin wata sanarwa da ya fitar a jiya Juma’a.

 

Sanarwar ta ce an kama mutanen ne a wata Harabar Kasuwanci da ke Unguwar Gudu a birnin na Abuja.
Oyewale jami’an hukumar sun kama mutanen ne a ranar 9 ga watan nan na Janairu.

Kakakin hukumar ya kara da cewa daga cikin wadanda aka kama sun hada da maza 67 da mata 38 cikinsu harda ‘yan Kasar ta China.

Acewar Oyewale bayan kammala bincike za a hukunta wadanda aka kama.

Leave a Reply

%d bloggers like this: