Gwamnan Jihar Akwa Ibom Umo Eno ya dakatar dukkan Kwamishinoninsa.

Gwamnan ya kori kwamishinonin nasa ne a jiya Juma’a a wani taro da ya gudanar, ya bayyana cewa ya sauke dukkan kwamishinonin nasa ne domin nada wasu sabbin mutane a cikin gwamnatinsa.

Gwamnan Eno ya bayyana cewa dukkan kwamishinonin nasa da ya dakatar, sun sauke nauyin da aka dora musu ta hanyar yin aiki yadda ake bukata.

Umo Eno ya kara da cewa a halin yanzu gwamnatinsa na bukatar sabbin kwamishinoni masu kwarewa a don ci gaba da tafiyar da gwamnatinsa yadda ya kamata, duba da cewa wasu daga cikinsu sun shafe shekaru Goma suna kan mukamin.

Sannan gwamnan ya kuma karrama dukkan Kwamishinonin nasa da ya dakatar a gurin wata liyafar cin abincin dare da ya shirya musu a jiyan.

Leave a Reply

%d bloggers like this: