Gwamnatin jihar Kano ta nuna jindadinta da hukuncin da kotun daukaka kara da ke Abuja ta yi na shari’ar masarautar Kano da ta shafi Sarki Muhammadu Sanusi II.

Babban layin gwamnatin Kano kuma Kwamishinan shari’a Barista Haruna Dederi ne ya bayyana hakan a yau Asabar a yayin ganawa da manema labarai.
Kwamishinan ya kuma bayyana hukuncin a matsayin babban nasara a bangaren shari’a.

Acewarsa Hukuncin da kotun daukaka kara da ke Abuja ta yanke ya soke dukkan hukuncin da babbar kotun tarayya ta yanke a baya, inda ya tabbatar da matakin da gwamnatin Jihar ta dauka akan al’amuran da suka shafi masarautar jihar.

Dederi ya kara da cewa hukuncin ya bayyana cewa gwamnatin Jihar Kano na yin aiki da gaskiya da kuma adalci tare da bin ka’idoji, wajen yin gyare-gyare a masarautun Jihar, da kuma kare al’adun jihar.
Dederi ya ce kotun daukakar ta kuma yi fatali da dukkan hukunce-hukunce da kuma umarnin da babbar kotun tarayya da ke Kano ta yi.
Kazalika ya kara da cewa dokar da Majalisar Dokokin jihar Kano ta yi akan masarautu da dukkan matakan da gwamnatin Jihar ta Kano ta dauka kotun ta tabbatar da su.
Sannan Dederi ya nemi da dukkan bangarorin da abin ya shafa da su mutunta hukuncin kotun.