Hedkwatar tsaro ta kasa ta bayyana cewa a cikin makon da ya gabata jami’an rundunar soji sun hallaka ‘yan ta’adda da dama tare da kwato makamai a sassa daban-daban na Kasar.

Mai magana da yawun rundunar Manjo-Janar Edward Buba ne ya bayyana hakan ta cikin wata sanarwa da ya fita.
Buba ya ce daga cikin nasarorin da jami’an suka samu akan ‘yan ta’addan sun hada da hallaka ‘yan ta’addan 120, yayin da suka kama wasu 105, tare da kubtar da wasu mutane 43 da aka yi garkuwa da su, a hare-haren da ‘yan ta’addan su ka kai daga ranakun 4 zuwa 10 ga watan Janairun nan.

Acewar Edward Buba jami’an sojin Operation Hadin Kai da ke aiki a yankin Arewa maso Gabas, ta hallaka ‘yan ta’adda 64 ta cikin wani hari da aka kai musu ta sama.

Har ila yau ya ce jami’an sojin sun kuma kamawa wasu mutane 28 da ake zargi da hannu a cikin ayyakan ‘yan ta’addan.
Kazalika ya kara da cewa jami’an Operation Fansar Yamma da ke yankin Arewa maso Yamma sun kai wani sumame kan wasu sansanonin ‘yan ta’addan, inda kuma suka samu nasarar hallaka ‘yan ta’addan 21.
Sannan ya ce sun kuma kama mutane 24 da ake zargi, sannan sun kuma kubtar da mutane biyar daga hannun ‘yan ta’addan.
Buba ya ce a yankin Arewa ta Tsakiya kuwa jami’an Operation Safe Haven sun kama ‘yan ta’adda 14 sannan sun ceto mutane 11 daga gurinsu.
Sannan Buba ya bayyana cewa jami’an sun kuma kwato makamai daban-daban ciki harda bindiga kirar gida guda uku da kuma harsasai 23, da dai karin wasu nasarori da jami’an suka samu akan ‘yan ta’addan.