Tsohon Kwamishinan ma’aikatar raya karkara na Kano Abbas Sani Abbas ya sauya sheka daga jam’iyyarsa ta NNPP zuwa Jam’iyyar APC.

Abbas ya sauya sheka daga jam’iyyar tasa ta NNPP ne a jiya Juma’a bayan gwamnan Jihar ya sauke shi daga kan mukaminsa na kwamishina.
Mataimakin shugaban Majlisar Dattawa Sanata Barau I Jibril ne ya karbi Abbas zuwa jam’iyyar tasu ta APC.
Sanara Barau ya ce za su aiki tare don ci gaba da ciyar da Jihar Kano gaba.

Daga cikin wadanda suka karbi Abbas Sani Abbas zuwa APC ciki harda shugaban jam’iyyar APC na Kasa Alhaji Abdullahi Abbas.

Abbas dai na daya daga cikin Kwamishinoni biyar da Gwamnan Kano Injiniya Abba Kabir Yusuf ya sauke daga mukaminsu.