Wasu ‘yan bindiga sun yi garkuwa da wasu mutane a lokacin da suka kai hari babban Asibitin garin Kankara da ke Jihar Katsina.

Maharan sun kai harin ne a cikin daren yau Laraba, inda kuma suka harbi wani likita mai suna Dr Murtala Sale Dandashire a yayin harin.

Rahotannun sun bayyana cewa maharan sun harbi likitan ne a ciyarsa, sannan suka yi garkuwa da mutane da dama a Asibitin.

A halin yanzu likitan ya na karba kulawa daga jami’an Lafiya.

Bayan faruwar lamarin jami’an tsaro sun bi sahun maharan domin kubtar da wadanda suka yi garkuwa da su tare da tsaron lafiya da dukiyoyin al’ummar yankin.

Leave a Reply

%d bloggers like this: