Rundunar soji ta Opration Hadin Kai ta haramta amfani da jirage marasa matuka a yankin Arewa maso Gabashin Kasar nan.

Kwamandan rundunar sojin Saman na Operation Hadin Kai Commodore U.U Idris ne ya bayar da umarnin daina amfani da jiragen ta cikin wata sanarwa.
Sanarwar ta bayyana cewa yin amfani da jirage marasa matuka ba tare da neman umarni ba, na haifar da babbar barazana ga Jihohin Adamawa, Borno, da kuma Yobe.

Idris ya kuam nuna damuwarsa bisa yadda hukumomin gwamnati da masu zaman kansu ke yin amfani da jirage marasa matukan, tare da neman umarni ba daga rundunar Operation Hadin Kai ba.

Sanarwar ta kara da cewa gudanar da amfani da jirage marasa matuka a wajen wasu harkokin ko kuma yin kasuwanci hakan babbar barazanace ga sha’anin tsaro, duba da rashin bin dokoki da kuma ka’idojin da bangaren ke dashi.
Idris ya bayyana cewa ‘yan ta’adda a Kasar suma sun kware wajen yin amfani da jiragen marasa matuka wajen kai hare-hare akan jami’an soji da kuma ababan more rayuwa a Kasar, inda ya ce koda a ranar 7 ga watan Janairun shekarar nan an kama wani fashinja a cikin jirgin wata kungiyar agaji daga garin Maiduguri zuwa Monguno da jirgi mara matuki a lokacin da ake gudanar da bincike a filin jirgin sama, inda aka kwace jirgin tare da ci gaba da gudnar da bincike kai.
Kwamandan ya ce hakan ne ya sanya suka haramta amfani da jiragen a yankin na Arewa maso gabas, inda ya ce dukkan wanda aka kama da karya doka zai fuskanci hukunci.