Jam’iyyar Labour Party na Kasa ta musanta Jita-jitar da ke cewa gwamnan Jihar Abia Alex Otti zai sauya sheka daga jam’iyyar zuwa jam’iyyar APC.

Sakataren yada labaran jam’iyyar na Kasa Obiora Ifoh ne ya musantan zargin a jiya Juma’a Abuja.
Sakataren ya ce babu wani shiga da Gwamna Otti yake na komawa jam’iyyar APC.

Jam’iyyar ta Labour ta musanta jita-jitar ne bayan bullar wasu rahotannin da ke nuni da cewa wasu daga cikin Gwamnonin Kasar na jam’iyyu adawa na shirin komawa jam’iyyar APC, sakamakon zaben Kasar da ke tafe a shekarar 2027 don samu nasara.

Daga cikin gwamnonin da aka ayyana za su koma APC sun hada, Alex Otti na jam’iyyar ta Labour a Jihar Abia, sai Siminalayi Fubara na Jihar Rivers a jam’iyyar PDP, Peter Mba na Enugu shima a jam’iyyar PDP, Umo Eno na Jihar Akwa-Ibom shima a jami’iyyar PDP ,sannan Sheriff Oborevwori na Jihar Delta shima a jam’iyyar ta PDP.

Dukkan kuma gwamnonin na kan wa’adin mulkinsu ne na farko, inda kuma suke neman sake darewa kujerun nasu a 2027 mai zuwa.

Bayan bayyana sunayen gwamnonin da ake kyautata zaton za su bar jam’iyyunsu, jam’iyyar ta LP ya cire sunan Otti daga cikin jerin gwamnonin za su koma APC.

A don haka jam’iyyar ta bukaci mutane da su yi watsi da jita-jitar barin Otti Jam’iyyar ta Labour duba da cewa jita-jitar ba ta da tushe balle makama.

Leave a Reply

%d bloggers like this: