Sanata mai wakiltar Borno ta Kudu sanata Ali Ndume ya bayyana cewa nazarin da gwamnonin Kasar nan suka yi akan kudurin dokar haraji abu ne mai kyau matuka.

Ndume ya kuma ce amma kuma hakan ba zai wadatar ba saboda akwai wasu bangarori na dokar da ya kamata ayi karin bayani akansu.
A hirarsa da BBC Sanatan ya bayyana cewa har yanzu ba su gama fahimtar wasu daga cikin dokokin gaba daya, inda suke neman karin haske akai.

Ndume yayi kira da a ci gaba da jin shawarwarin mutane, tare da tattaunawa don ganin an samar da gyare-gyare akai, duba da cewa idan aka gaggauta aiwatar da shi za a yi babban kuskure.

Acewarsa ‘yan majalisa da al’umma ne ke da alhakin samar da gyara kurakuran da ke cikin sabbin dokokin a yanzu.